Part 75

564 18 0
                                    

❤❤💋💋
IHSAN
❤❤💋💋

(Romantic, Love,Sorrow)
❤❤💋💋💫💫🌟🌟

Written By✍🏻
Khadeejaht Hydar .
Young Novelist.

✍✍✍✍✍✍✍✍
GOLDEN PEN WRITER'S ASSOCIATION
✍✍✍✍✍✍✍✍

❄We are bearers of sooo golden a pen.
We write assidiously percieven no pain
Sooo magical.
Our creative golden pen,
Be hold our words.
A product of our pen
Savour our words, for it will cause you no pain.❄

Dedicated to.
Muhammad Angon Anti fauziyya Allah yakaimu kd musha biki.Amin.

I love ur comment fans I love u to death.

7⃣5⃣
Suna zuwa ta zauna saboda Sam jikinta babu kwari,Angel tace".... Sis mezakici? tace".....no karkidamu zan dafa indomie, Fatima tace".... Haba Sis ai anzama d'aya ai larura ce tasa karkiji nauyin wai zamu miki girki kifad'a kawai.

Murmushi tayi tace".... D'an wake zanci,Angel yace".... Anti Fatima bara baje nayi tafad'a tare da tashi Fatima ma tabi bayanta.

Deen Wanda yaji an ambaci d'anwake ya b'ata fuska,zama yayi a kusa da'ita yace".... Haba wifey mezakiyi da d'an wake kuma kamar zatayi kuka tace"..... Ni shi nakeso,ganin tana b'ata fuskane yasashi cewa to aci lfya  tace".... Kaifa yace"... A'a daganan ya koma gunsu Fahad itakuma ta wuce gunsu Angel.

Cikin minti talatin suka had'a d'anwakensu mai rai da lfya Wanda yaji su cabbage da tumatir da manja ga yaji,haka suka jera a dining suka dawo parlour don k'iran mazajennasu.

Kowa ya hallara a dining d'in banda Deen,Ganin baida niyyar zuwane yasa ta zuba musu ita dashi tace".... Kuci abincin ni ak'asa zanci."

Gabanshi ta ajiye kwanon d'anwaken tace"...... Hubby muci yace"..... Wifey plss kici kinga magriba takusa kici kisha magani kinji.

Kuka tafara masa kan lalle saiyaci ganin yadda takeyi kuma ya tuna da maganar doctor na cewa kar a b'ata mata rai,haka yasa hannu suka fara ci sai kallon yadda takeci yake.

D'ag'owa tayi taga ko d'aya baiciba yasata fara alamun kuka,ba shiri yakai bakinsa  yafara taunawa jin yadda abinke masa a baki yasa yafara kok'arin hararwa.

Saurin rufe masa baki tayi tace".....plss ka cinye karka zubar haka ya had'iye,Me su Fahad zasuyi inba dariya ba suka dingayi har saida Deen ya jiyo ya hararesu."

Fahad  yace".... Khadeeja zatayi saurin sauyawa fahad ra'ayi,Angel tace".... Allah inaganin cikintane ke sata wannan rigimar.

Haka suka kammala Angel ta tattara kayan  ta kai kitchen ta wanke ba yadda Ihsan batayiba don tayata amma tak'i,Band'aki ya shiga yafara kwarara amai saida ya amayar tass sannan ya bud'e fridge d'in d'akin ya d'auki yoghurt yasha ya fito.

Yana fitowa Fahad yace".... Bature yakaji d'anwaken ne,Bansaniba ya bashi amsa dariya suka saka daganan mazan suka nufi masallaci.


Bayan sun tafine Angel  tace".... Plss sis kina kok'arin Koyama Yaya cin  abincinmu na hausawa,Fatima tace".... To Allah yasa ya'iyacin miyar kuka  dariya Angel tayi tace"..... Na tuno lokacin da mukaje kauye akabamu miyar kuka yaya nagani wani kashin jariri ne.

Dariya sukayi dukansu Fatima tace"..... Kiyi amfani da cikin jikinki kawai ki koya masa tunda naga bayason b'acin ranki d'azuma hakanne yasashi ci inba hakaba wlh bazeciba."

❄❄❄❤❄❄❄
Tace"....Insha Allah,Daganan sukayi sallah suka zauna suna azkar har aka k'ira isha'i bayan sun idarne suka fara shirin tafiya.

Su Deen ne suka shigo kowa d'auke da leda a hannunsa,sallama sukayiwa juna kowa ya wuce b'angarensa da Queen d'insa a gefensa.

Bayan sun gama nafilolin da suka saba da daddare kafin su kwanta, ta shirya as usual cikin kayan baccinta Riga iya kneels dinta sai dogon wando masu santsi farare.

Gado ta haye tayi kwanciyarta bayan tayi addu'a ta shafe jikinta,shima addu'a yayi ya kwanta tareda jawota jikinsa.

Saurin tashi tayi tana turo baki kallonta yayi yace"....what wifey?tace.... Banaso yace".... Bakyason me tace".... Kana tab'ani tayi maganar tana son sauka daga jikinsa.

Be saketaba illa bakinshi dayake niyar kaiwa nata,gefe tayi da fuskarta tayi saurin tashi tare da fashewa da kuka.

Kallonta ya tsaya yi ,don ya fuskanci tanaji da shagwaba yace".... To shikenan zo mu kwanta,kwanciya tayi kusa dashi kwantawa shima yayi yana jimamin yadda zasu kaya  intace haka zasu kasance.
[1/24, 9:10 PM] Khadeejaht hydar Novelist:

IHSANWhere stories live. Discover now