uncle naseer

234 27 5
                                    

Part 37&38
💓💓💋❤️

.....nuni sultan yay mai da kujerar karfe dake gefen hajjo....memakon ya zauna akai  ,sai yay zaman sa...a kasan carpet din......tashi jakadiya tai bisa umarnin da sultan yabata na kulle curtains din dakin....
Tana kammala rufewa tai ficewarta daga dakin....

Gyaran murya sultan yay... sannan yakira sunan sa"Naseer " yafada yana me kafe shi da idanu....dagowa yay sannan ya maida kansa kasa,yana me amsa kiran da sultan yay masa...batare da yabari sun hada ido ba,saboda kwarjinin dake tattare da idon sultan din....

"Nasan a yanzu zuciyarka cike take da wasi wasin da lilin kiran da mukaima...?"

Sultan yafada yana me dauke idanunsa daga kan naseer ,don basa damar yin magana....

"Eh..!"...yafada muryanrsa na rawa...

Dan murmushi sultan yay irin nasu na manya kafin yadora da fadin.....

"Bakomai ne yasa na kiraka ba face don bayyana ma,kaso daya cikin ukun sirrin da muke boye ma"

Dan jimmm sultan yay ... sannan yakira sunan hajjo ..."fulani"...yana meyimata nuni da wata tsohuwar akwatin karfe dake gefenta.....tashi hajjo tai ta nufi...inda akwatin take....

Tana zuwa ta dakkota kasancewar bawata babba bace...
A kan tebir din katakon dake gaban sultan ta ajjiyeta..

Nuni yay mata da ta bude akwatin,...budewa tai ...umarni sultan yakarai bata data dakko abun dake ciki....dukka hannayenta biyu tasa ta zaro  dan madaidaicin allon dake cikin akwatin .....

Nuni yay mata da uncle naseer ,da kansa ke a sunkuye,zagayawa tai tagefen sultan ta mikawa ,ta mikawa uncle naseer allon sannan ta nemi waje ta zauna....

Gyaran murya sultan yakarayi a karo na biyu sannan yafara bude taron nasu da addu'a..

"Nasani naseer ,kanka kara kullewa yake fiye da sanda kashigo nan wajen,toh kah kwantar da hankali n ka ,don bazaka fita daga dakin nan ba,harse na warware ma kaso arba'in 40% cikin 100% na rudani da kake ciki,yayinda sauran saidai mu barwa,ubangijin da yatsara komai ya warware su a duk lokacin da  yatsara wanzuwar hakan"...

Yafada yana me yin gyaran murya...

Hajjo ce tafarayin magana tana me share hawayen daya fara zubo mata...

*Naseer inason kasani,kai din, Dane da Allah ya saukar dashi amatsayin aya ga magauta da  maguna  masu  kwanciyar daukan rai ,na gidan nan,wanda suma kansu masu bacci da ido daya na gidannan sun shaida haka..duba da  haihuwar ka,...."

Gyaran murya sultan yakarayi yiwa hajjo...sanin me yake nufi yasa hajjo ..

Dakatawa daka cukurkudaddun maganganun da ta faro....

Duban shi tasake yi tana me kawar da dukkan raunin da ya ziyarceta,da kuma  famin tsohon   ciwon dake ranta shekara da shekaru da zatayi.....

"Naseer inaso kadauki tinaninka ka maidashi kimanin shekara talatin da bakwai 37 years da suka wuce.....
....

Alif dubu daya da dari tara da  tamanin da hudu 1984

Kota ina kaduba a cikin  babban filin gidan sarautar zazzau ..da aka ware don gudanar da hawan sallah,kokuma idan sarki zaiyiwa alumma wa'azi idan an an idar da sallar juma'a. ..,cike yake da baki babu matsakar tsinke... yayinda bayi da kuyangin gidan..suke ta faman kai-kawo. Ka caaa suruta jama ta ko ina..kakeji ta ko ina sekace ran sallah,jama'a kwa kama daga talakawan gari masu kudi da kuma bakin da masarautar tasamu kowa kaduba zakaga cikin murna yake fuskarsa dauke da murmushi....

Can saman benen gedan sarautar kuwa  sultan ne zaune  ,,da fadawnsa be,se wazeeri dake gefensa... sekuma   baffansa ,galadima a gefen sultan na hagu.. wanda ya kasance  kanin babansane .....

UNCLE NASEER  ✅Where stories live. Discover now