uncle naseer

275 44 9
                                    

Part 49&50
💓💓💓💋
Happy birthday to you diver , you have no idea how much you mean to me I really like you you're an amazing inspiring motivator to me have a fabulous celebration💓💥💋.23/1/2022

...... Abdul Naseer ne zaune a acikin dakin sultan, yayinda adaya gefe kuma hajjo ce zaune akan daya daga cikin kujeran dakin......anan suke haduwa batare da kowa yasani ba,kan abubuwan da suka shige musu duhu..

Kamar kullum tattaunawarsu sukeyi ta sirri, sultan na lure da Abdul Naseer yanda yakasa nutsuwa tinda aka fara tattaunawar,..dan bini bini yake dafe kansa da hannunsa,..ganin hakanne yasa sultan bawa hajjo umarnin ta kamashi su tafi can Bangaren sa da ita.....ya kwanta

Acan Bangaren kuwa mufeeda ce keta faman kiciniyar kwacewa daga shakar da akai mata ta baya,batare datasan kowanene ba.....zarata. Farata masu tsini dake hannunsa kawai take iya gani ,bako ina yake kokarin caka da faratan nasa ,ajikinta ba face cikinta... addu'oi tafara karantawa tana tofa mai,duk da batasan namiji ne koh mace neba,abu daya kawai ta fahimta shine kamar ba mutum bane yay mata wannnan shakar duba da irin ihun da yake kurmawa aduk lokacin da yawun adduar ta ya sauka ajikinsa,amma duk da haka be saketa ba se ihu da kiran ..."se kin bani! Sekin bani duhana!!!..zan cika miki alkawarin ki sena cika!,miki alkawarin da na daukar miki,sena farka cikin ta na dakko! Dam tayin nakawo miki kin meda meitar ki ,sena yi!"

Aka karashe fada cikin wata kakkaurar murya mara dadin ji,...
Hannu guda shedanin! Yas ya bayan ya shammaci mufeeda ya doka ta da kasa .. sannan yasa daya daga cikin faratan hannunsa ya janyo gashin kanta,ta silar janyowar da yay seda gashin ta yabar kanta ..hannu ya kuma sawa ya dagota buga kanta yay da bango,jinin da yaga yana zilaloewa ta bakinta da hancinta.yasa hannunsa ya laso yakai kan bakinsa sannan ya takarkare ya kwarara wani siririn ihu yana me cewa.." hakika dole ne ,ki mutu dole ne ki mutu ,ashema biyu ne huu!"

Duk wadannan surutun da wannan shedanin yakeyi.. mufeeda na jinsa amma sama sama,don tin bugawar da yay mata a farko ..tafara ganin dishi dishi,amma saboda bakin naci da san cikar alkawarin da ta daukarwa kanta,nason ganin wanene yasa take dorewa...

Cikin zafin nama da dan sauran kuzarin da ya rage mata ta ,ta wara yatsunta duka tana me karanto ..."la'ilah! Ha illa antha subhanaka! Inni kuntum minazzalimun!"

Takaai adduar tana me soka mai yatsunta acikin kwayar idonsa hadi da tofa mai ruwan adduar..afuskarsa ihu yasaki yana me sakinta tafadi a kasa ...

Kara durfafarta yay haikan yana me wara yatsunsa da nufin farka cikinta... zuwa wannan lokacin mufeeda ta saddakar don dan karfin nata ma ya dauke,gakuma wani irin sarkewa da makogaronta yay hadi da bakinta da ya daskare yakasa motsi ahankali jinta da ganinta ya dauke cancarakat!

Jin alamar ana durfafo falon ne, yasashi dakatawa daga yunkurinsa na son ciro dan cikinta ....

Tabbatarwar da yay nan ake kokarin shigowa yasashi .. saurin ratsawa ta jikin bango ya fice..

Hajjo da uncle naseer da karasowar su kenan cikin dakin... saurin dakatawa hajjo tai , sakamakon yin tuntube da tayi da abu saurin kai dubanta tai wajen..,aibatasan sanda ta saki Abdul Naseer ta zube akasa tana me tallafo mufeeda kan cinyarta ,ga baki daya ta rude tarasa ma me zatai wazata kira ...ihun da hajjo tasa ne ya ..yay daidai da daidaituwar kwakwalwar Abdul Naseer da ,ya fice a hanyacinsa tin a Bangaren sultan......

Amatukar gigice ya zube adaidai inda hajjo ke dauke da mufeeda yay..yana mesa hannunsa yajawota jikinsa ya kankame ,

Ganin haka yasa hajjo fice cikin tashin hankali ... hada hanya kawai takeyi kafafunwanta ba ko takalmi , kasancewar da alkyabba ajikinta yasa ba agani,amma sukansu dakarun dake gadin Bangaren mufeeda sun fahimci ba lfy tindaga hucewa da hajjo tai da Abdul Naseer ba a hayyacinsa ba kama daga karar data kwala zuwa yanzu da tafito afu jajan...

Kallon kallo kawai suke ta faman aikawa junansu hadi da tambayar juna koh lfy.....

Sultan na zaune ayanda su hajjo suka barshi,segata tadawo .. yanayin da yaganta kadai ne ya tabbatar me ba lfy ba don shi atinaninsa jikin Abdul Naseer din ne ya rikice....bayyi wata wata ba suka nufi Bangalren uncle naseer din shida hajjo ,ta kofar sirrin da Abdul Naseer yake bi yaje wajen da suke haduwa dasu sultan da hajjo,tanan sultan yabi. Suka karaso Bangaren Abdul Naseer....

Yana zaune akasan carpet kunkume da mufeeda a kirjinsa yana shafa mata ruwa a fuskarta..amma ko motsi batayi...

Jin andafashi ne yasa ya juya don ganin waye,da hannu sultan ya dagoshi hadi daimai nuni da ya kwantar da hankalinsa zata farfado.....

Nan sultan yasa hajjo ta samo zam zam yay adddua aciki sannan ya shafawa mufeeda a fuskarta ....

Wani kalar gurnani ta hauyi ,hadi da bige bige hannunta sultan yasa Abdul Naseer ya ya hade waje guda ya rike da karfi sauran ruwan zam zam din ya karba a hannun hajjo ya zuba mata a baki...batafi minti daya 1 da farasha ba , ta fara dawo dashi..can kuma sega wani kalar koren ruwa sharr yafara biyo bayan ruwan zamzam din daga koren ruwan se jini...nan da nan sega jini ta hanci da baki kunne gabaki daya hankalin hajjo da Abdul Naseer ya tashi ganin halin da mufeeda takeci..nan take hajjo tafara kwalla... sultan kansa seda ya tausaya mata,don shikansa yataba dandana shiga irin halin da take ciki farkon hawansa mulki,ba komai bane wannan abun da mufeeda takeyi face aiki na magauta.....

Ahanzarce sultan ya nufi Bangaren da sa ta wannnan kofar dai da yabiyo,hajjo data fahimci ba abun na gaske ne yasa tai saurin fita waje ta bawa dakarun tsaron wajen umarnin kar su kuskura su bar wani ya tako ko barandar Bangaren, sannan ta dawo ta rufe kofar falon daga ciki...bayan kamar mintuna 20 hajjo dake zaune taji an yi knocking kofar data kulle,tai saurin zuwa tabude batare data tambaya ba, jakadiya ce hannnunta ta dauke da wata katuwar kwarya.... ta shigo .. hajjo dataga bataga sultan ba yasa ta tambayar jakadiya,nan ta gayamata yana Bangaren sa,....yace kuma yanasone ganin Abdul Naseer ...nan da nan Abdul Naseer batare da bata lokaci ba,yabi ta kofar da sultan yabi ya fita, yana rufewa jakadiya taje ta maida lokar dake wajen yanda take.....

Durkusawa jakadiya tai sannan tace,"ranki yadade sultan yabada umarnin kar abari maganar ciwon shatu ya bayyana ga kowa...."

Jakadiya tafada tana me mikewa ta dauki kwaryar dake gabanta ,ta nufi inda mufeeda take...

"Da kindauke kinkaita dakinta ,inyaso koma mene ne se ayi can kmr zefi sirri"

"Ranki yadade yanda kikace haka za ayi"... jakadiya tafada Tana me ciccibar mufeeda itakuma hajjo ta daukar mata kwaryar sukayi dakin ta....

Bayan bakar wuyar da su hajjo suka sha akan mufeeda ,ansamu ta farfado....ammma sedai tinda ta farka babu abunda takeyi se aikin kalle kalle kawai,tai ziru ba uhmmrbare uhmm, hankalin hajjo yatashi ganin duk yanda za ai tai magana anyi takiyi... ganin halin da hajjo ke ciki ne yasa jakadiya sunkuyar dakanta tana me cewa...

"Ranki yadade ki kwantar da hankalinki,dama ba lallai bane tayi magana daga tashinta ba,mubarwa yamma koh gobe agani,"

Hmm!

Hajjo tace tana cewa
"Mungudewa Allah da cikin jikinta ma be bare ba!"

"Allah abun godiya" inji jakadiya

"Anya mutane gidannan kirazansu akwai Allah, su rasa akan wanda zasui mugun abunsu se yar talikiya dabatasan hawa ba batasan sauka ba ," hajjo ta fada tana me share kwallar da ta zubo mata...

" Allah zekawo karshen komai ,kibadade koh bajima"cewar jakadiya....

_______________________________
Tindaga wannan abu da ya faru Abdul Naseer be kara yarda yabar mufeeda ita kadai ba,koh nan da can baya barinta taje sedashi..har izuwa lokacin da ta fara nakuda a tsaitsaye .....✍️

Inshallahu a chapter gaba zamu gaba wannan tarihin adawo ainahin labari....marasa votting kuci kanku masuyi inah godiya alkhairin Allah yakai muku aduk inda kuke.. ameen thumma ameen kai harda ku marasa votting din...don girman Allah wanda kuhkoma tindaga fejin farko kuih votting please rokanku nai danku seda roko 😏🤣💓



UNCLE NASEER  ✅Where stories live. Discover now